Kalaman Soyayya Masu Dadi

Duniya tana da fadi kuma kowa da irin baiwar da allah ubangiji yayi masa akwai mutane da dama wadanda furta kalaman soyayya masu dadi bakomai bane abakinsu. Wasu kuma furta kalamai masu dadi zuwaga abinda suke so wahala yake basu.
Dan haka karka wani damu idan har baka iya wani abu a wannan duniyar ba, domin kuwa bada shi aka haife mu ba. Saboda duk wanda kaga ya iya wani abun toh koya masa aka yi.
Amma wani lokacin ana iya samun yanda wani zai fahimci wani abu dawuri wani kuma sai anta koya masa sannan zai fahimta.
Wannan shine dalilin dayasa mukaga yadace mu koyawa wasu daga cikin mutane wadanda basu iya kalaman soyayya ba. Dan haka yanzu zamu nuna muku hanyoyi kala-kala da ake iya tsara zance mai dadi zuwaga abinda mutum yake so.
Kalaman Soyayya Zuwaga Budurwa
- Bantaba tunanin a duniyar nan akwai wata ‘ya mace da zata iya sauyan rayuwa nadawo ina jin dadi ba sai ke, Saboda nakasance abaya ina rayuwa cikin kunci da rashin jin dadin duniya amma sai gashi lokaci daya duk kin canza komai.
- Qanwata ina sonki kuma wllh banga wani abu a duniyar dazan iya yimasa irin son da nake miki ba, domin duk wani farin ciki da nake a yanzu kece sila dan haka babu abinda bazan iya mallaka miki ba.
- Tun lokacin da muka fara haduwa dake zuciyata take cemun kada nasake nayi wasa dake aikuwa tunda naji zuciyata tafara rayamun irin haka nasan nayi dacen budurwa mai mutunci kuma yar gidan mutunci.
- Nifa tunda nake a rayuwata banta jin wata ‘ya mace mai dadin muryarki irin taki ba yar gidana. Saboda ni a yanzu nadaina jin dadin muryar kowace ya mace idan ba taki ba.
- Ni yanzu gabakidaya kindawo dani makawo domin zan iya cewa nadaina ganin kyawu na duk wata ya mace idan ba naki ba yar gidana. Shine ma dalilin dayasa idan muna tare zakiga inata kallonki saboda irin kyau da Allah ubangiji yayi miki.
Kalaman Soyayya Zuwaga Saurayi
- Yayana bakasan me nakeji akanka ba wallahi narasa me yake damuna tun lokacin daka rike hannuna komai nawa ya canza. Dan Allah ina neman alfarma daya a wajenka idan har zan samu, inaso duk lokacin da kasake zuwa gurina zance inaso kasake rikemin hannuna da wannan hannayen naka masu laushi sai kace katifa domin natabbata hakan zai kara sani farin ciki.
- Tunda nake a rayuwata yayana bantaba haduwa da saurayin da muka dace da juna ba wanda bana jin shayin nunawa yan uwa shi ba saikai wallahi shiyasa tun yanzu nake neman alfarmar duk sanda Allah yasa mukayi aure inaso idan zamuje unguwa mudinga jerawa tare hakan zaisa nasani farin ciki mara musaltuwa.
- Yayana anya kuwa bazan dawo boyeka ba domin tun lokacin da qawayena suka fara ganinka naga duk sun kidime sunata maganarka. Ni yanzu dan Allah idan zakazo wajena kadinga saka Face mask kada yan mata sudinga gane mun kai.
- Kai ne mutum nafarko yayana dayaci nasara akan zuciyata saboda duk wani abu da take bukata tana samu a wajenka, Bani da wani abu dazan iya biyanka dashi saidai kawai nace Allah yabani kai amatsayin mijina domin nasan kamar yanda kabawa zuciyata kulawa nake farin ciki nasan haka zaka bani kulawa.
- Yayana saboda irin farin cikin da kake sakani da ace zan iya wakiltar kaina a matsayin wacce zata iya jagorantar daurin aure da wallahi nawakilci kaina dani dakai andaura mana aure.
Wadannan sune kadan daga cikin kalaman soyayya masu dadi wadanda muke ganin zasu iya taimaka muku wajen cin nasarar sace zuciyar abinda kukeso. Amma a kowane irin lokaci zamu iya canza wasu daga cikin kalaman soyayyar da suke nan.